Taɓa Ka Lashe

Shirin Taba Ka Lashe yana gabatar da bayani cikin sauƙi da Hausa kan muhimman abubuwa kamar cryptocurrency, blockchain, da fasahar zamani.

🟨 Gabatarwa:

Jama’a, Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Suna na Sabiu, barkan ku da zuwa Kainuwa.
Barkan mu da saduwa a cikin sabon shirinmu mai suna TAƁA KA LASHE.

Shirin Taba Ka Lashe an tsara shi ne domin kawo muku ilimi mai amfani cikin sauƙi da yaren Hausa, musamman akan batutuwan da suka shafi:

  • 🔹 Cryptocurrency
  • 🔹 Blockchain
  • 🔹 AI (Artificial Intelligence)
  • 🔹 da sauran fasahohin zamani da suka shafi rayuwar yau da kullum.

Taɓa ilimi — lashe romon amfaninsa.
Taba Ka Lashe – ilimi mai amfani cikin gajeren rubutu da gajerun bidiyoyi.

Za ku iya kallon shirin Taba Ka Lashe a dandalinmu na:


📺Taɓa Ka Lashe  – Crypto Series 1 (tklcs1)

 

🟨 (tklcs1) Episode 1:

Menene Cryptocurrency?

A taƙaice, cryptocurrency kuɗi ne na yanar gizo kaɗai. Ma’ana, ba a ganinsa a zahiri kamar takardun kuɗi ko tsabar kuɗi – ana amfani da shi ne ta hanyar intanet kawai.

Babu wani mutum guda ko ƙungiya — gwamnati, banki ko kamfani — da ke sarrafa ko juya akalar cryptocurrency kai tsaye. Wannan yana nufin cewa babu wanda zai iya hana ka amfani da shi kai tsaye.

Duk da haka, akwai ƙalubale da ƙa’idoji a wasu ƙasashe da ba za a rasa ba.

Bitcoin daya ne daga cikin dubban cryptocurrencies na gaske da mu ke da su a yau, kuma shi ne jagoran tafiyar.

🔹 Kalmar “cryptocurrency” ta fito ne daga haɗin kalmomi biyu:
Cryptography da kuma Currency

✅ Tsakure (Takeaway):

  • Cryptocurrency: Kuɗi ne na intanet.
  • Babu hukuma guda da ke sarrafa shi.
  • Kalmar na nufin tsaro (cryptography) + kuɗi (currency).


🟨 (tklcs1) Episode 2:

Asalin Kalmar Cryptocurrency?

Kalmar “cryptocurrency” ta samo asali ne daga haɗin kalmomi biyu:
Cryptography da kuma Currency

💸 Currency

Kuɗi ne da ake amfani da su a kasuwanci da cinikayya — irin su naira, dala, riyal da sauransu.
Su ne kuɗaɗen da muke amfani da su a rayuwar yau da kullum, kuma ana kiran su da suna fiat money.

🔐 Cryptography

Hanya ce ta ɓoye bayani ko saƙo ta yadda ba wanda zai iya fahimta sai wanda aka nufa da saƙon.

🛡 Amfanin Cryptography a cikin Cryptocurrency

Ana amfani da private key da public key don kare kuɗi da tabbatar da tsaro a mu’amaloli wato transactions.

✅ Tsakure (Takeaway):

  • “Cryptocurrency” = Cryptography + Currency.
  • Tsaro yana cikin asalin tsarin kuɗin intanet.


🟨 (tklcs1) Episode 3:

Sirrin Private Key, Seed Phrase da Public Key

🔐 Private Key

Wannan wasu jerin lambobi da haruffa ne a haɗe — wato alphanumeric (alfanumerik)

Shi ne sirrin da ke ba ka damar aikawa da kuɗi ko saka hannu wato signing a transaction cikin tsaro.

Kamar ATM PIN ɗinka ne — kai kaɗai ya kamata ka san shi.

🎁 Seed Phrase (Secret/Recovery Phrase)

Wannan jerin kalmomi 12, 18 ko 24 ne da ke wakiltar private key ɗinka a hanya mai sauƙi.

Manufarsu ɗaya ce da private key: su ne ke baka cikakken iko da wallet ɗinka da kuɗin da ke cikinta.
Ba a yarda a bawa kowa ba!

❌ Duk wanda ya tambaye ka seed phrase ko private key — scammer ne.
SCAMMERS — Barayi ne.

🔓 Public Key

Shima alphanumeric code ne — amma ana mayar da shi wallet address ta hanyar abin da ake kira hashing, don haka sabo da saukin fahimta, da public key da wallet address mu dauka duk abu daya ne.

Wannan shine adireshin da mutane ke amfani da shi don tura maka kuɗi.

Kamar lambar asusun banki ce — ana iya rabawa da jama’a, ba sirri ba ne.

✅ Tsakure (Takeaway):

  • Private key/Seed phrase = Sirri ne, ba a bawa kowa
  • Public key = Ana iya rabawa ga kowa don turo crypto


🟨 (tklcs1) Episode 4:

Menene Blockchain?

An ƙirƙire cryptocurrency ne bisa fasahar  blockchain.

Blockchain wata fasaha ce ta ajiye bayanai a bayyane ga kowa, kamar littafin rijista ne na jama’a inda ake rubuta kowace ma’amala (transaction), tare da kwanan wata, lokaci da adadi. Kamar dai yadda littafin bayanan banki ya ke, sai dai ita blockchain kowa zai iya ganin komai.

Babu hukuma guda da ke sarrafa shi — kowa na iya dubawa amma ba kowa zai iya gyarawa ko ba.

✅ Tsakure (Takeaway):

  • Blockchain = Tushen tsari na cryptocurrency.
  • Littafin adana bayanai ne da kowa ke iya gani, ba a iya canza shi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *